Tuesday, 2 December 2014

Gwamnatin Nigeria ta musanta zargin da wasu ke yi cewa tana da hannu a hare haren da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a arewacin kasar.


Mataimakin shugaban kasar Arc. Namadi Sambo wanda ya futo daga yankin arewacin ya ce babu yadda 'yan yankin da ke cikin gwamnati musamman a fannin tsaro za su bari a yi wani abu da zai cuci al'ummarsu.
Namadi Sambo dai na magana ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin kasar a ziyarar ta'aziyya da
jaje da suka kai Kano, sakamakon hare haren da aka kai ranar Juma'ar da ta gabata.
A nasa bangaren, sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi na biyu ya yi kira ga gwamnatin kasar da a gano masu hannu a hare haren ta hukunta su.

No comments:

Post a Comment